– ‘Dan wasa Pierre-Emerick Aubameyang ya jaddada aniyar sa na bugawa Kungiyar Real Madrid.
– ‘Dan wasan na Kasar Gabon yayi wa kakan sa alkawarin cewa, sai ya bugawa Real Madrid kwallo wata rana.
– Kungiyar Man City da Inter Milan sun nemi a saida masu dan wasan, sai dai Borussia Dortmund sun ce ba na saidawa bane.
Dan wasan gaban nan Pierre-Emerick Aubameyang na Kungiyar Borussia Dortmund yace yana fa so ya bugawa Kungiyar Real Madrid kwallo.
Dan wasan gaban Borussia Dortmund, Pierre-Emerick Aubameyang ya kara tabbatar da muradin sa na komawa Kungiyar Real Madrid da buga kwallo. Dan wasan gaban mai shekaru 27 ya dade yana son ya bugawa Kungiyar Real Madrid Watau ‘Los Blancos’ kwallo.
Dan wasa Pierre-Emerick Aubameyang ya bayyanawa Kungiyar sa ta Dortmund cewa, idan har Real Madrid suka zo neman sa, to zai tashi. Rahotanni sun nuna cewa dan wasan mai cin kwallo ya taba yi wa kakan sa alkawarin cewa wata rana zai buga kwallo a Filin Santiago Bernabeau na Kungiyar Real Madrid a rayuwar sa.
KU KARANTA: Arsenal na neman Miguel Almiron
Duk da cewa maganar komawar sa ko neman na sa bai yi karfi ba, amma dan wasan ya ce burin sa a rayuwa ya dai gan sa cikin farar rigar nan ta Real Madrid. Duk da cewa an kusa rufe kasuwar sayayyen ‘yan wasa dan wasa Pierre-Emerick Aubameyang bai cire rai da komawa Kungiyar ba.
Kungiyar tana da masu cin kwallo irin su: Alvaro Morata da kuma Karim Benzema yanzu haka, sai dai idan har Kungiyar ta Real Madrid za ta saida daya daga cikin ‘yan wasan ta kamar Isco ko kuma James Rodriguez to akwai tsammanin ta saye dan wasa Pierre-Emerick Aubameyang daga Dortmund.
Kungiyar Dortmund dai ta yi watsi da tayin Manchester City da kuma Kungiyar Inter Milan da suka yi kokarin sayen dan wasan. Kungiyar tace Kyaftin din Kasar Gabon din Pierre-Emerick Aubameyang bana saidawa ba ne.
Leave a Reply